An Rushe Shugabancin Jam'iyyar APC A Kowane Mataki

Daga Muhammad Farouk 

Majalisar ƙoli ta jam'iyyar APC ta rusa dukkanin kwamitocin shugabancinta a matakin ƙasa da ma yankuna da kuma jihohi. Haka zalika an rusa kwamitin shugabancin riƙo na ƙasa ƙarƙashin shugabancin Gwamna Mai Mala Buni na Yobe a zaman da majalisar ta yi bisa jagorancin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a Fadar Aso Rock Villa a yau Talata.

Sai dai duk da rushe kwamitin na shi, gwamna Mai Mala Buni an sake naɗa shi domin ya ci gaba da jagorancin kwamitin na tsawon wata shida nan gaba.

Haka zalika, majalisar ta kori Ntufam Hilliard Eta, tsohon mataimakin shugaban APC na yankin kudu maso kudu, daga jam'iyyar saboda ya ƙi janye ƙarar da ya shigar da jam'iyyar a gaban kotu yana neman ta ayyana shi a matsayin shugaban jam'iyyar na ƙasa.


Post a Comment

0 Comments