An Taso Keyar Maina Daga Nijer Zuwa Nijeriya



Daga Muhammad Farouk 

Abdulrasheed Abdullahi Maina, tsohon shugaban Hukumar Fensho ya iso Nijeriya bayan da aka taso keyarsa daga jamhuriyyar Nijer. 

An dai cafke Maina ne a ranar 30 ga watan Nuwamban 2020 bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo. 

An taso keyarsa ne zuwa Abuja bisa wakilcin ‘yan sandan kasa da kasa da kuma ‘yan sandan Nijeriya. 

A ranar Talata ne ‘yan sandan Nijeriya suka ce suna aikin wajen ganin sun dawo da Maina Nijeriya bayan da suka cafke shi a birnin Niamey. 

Maina dai ana zarginsa da laifuffuka daban-daban. Inda EFCC suka ayyana shi ruwa a jallo bisa laifukan da ya hada da zambo da kuma makirci. 

Sakamakon tserawar Maina, an daure Sanata Ali Ndume wanda ya tsaya masa a zaman kotu na karshe.


Post a Comment

0 Comments