Ana Zargin Jarumar Fim Din Indiya Da Rataye Kanta

 


Jarumar Fina-finan Indiya mai suna VJ Chitra rahotanni sun ce ta kashe kanta a dakin Otel din da take dake wajen garin Chennai da safiyar ranar Laraba.

Jami’an ‘yan sandan Tamil sun ce suna zargin ta kashe kanta ne bayan da aka samu ‘yar wasan a rataye a dakin Otel din da take.

‘Yar wasan dai ta shahara a fim din ‘Pandian Stores’.

Sai dai dangane da mutuwarta, har yanzu a hukumance ba a tabbatar da hakikanin abin da ya kashe ta ba. Tuni aka mika gangar jikin Chitra domin gudanar da bincike na musamman.

Har wala yau Chitra ta kasance ‘yar jarida ce a gidan Talabijin na Tamil TV.

Post a Comment

0 Comments