'Annobar Korona Zai Jefa Sama Da Mutum Miliyan 32 Cikin Matsanancin Talauci'

 


Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa adadin mutanen da suke fama da matsanancin talauci zai karu zuwa sama da mutum miliyan 32 a shekarar 2020 sakamakon annobar cutar korona da ake fama da shi. 

Wannan bayanin na dauke ne a cikin rahoton sashen taruka da cinikayya da kawo ci gaba (UNCTAD) na majalisar dinkin duniya na ranar Alhamis. 

Bayanai sun nuna cewa cutar annobar korona ya durkusar da tattalin arziki musamman ga kasashe masu tasowa, inda lamarin ya fi shafar talaka.

Post a Comment

0 Comments