Batanci Ga Annabi (S): Kamfanin Faransa Na Fuskantar Durkushewa?


Daga Madogara TV 

Jaridar Bloomberg ta labarto cewa; kamfanin Danone na kasar Faransa na shirin rage ma’aikata dubu biyu (2, 000) a wani mataki na adana zunzurutun kudin da ya kai dala biliyan 1 da miliyan 200. 

Daga cikin ma’aikatan da kamfanin zai rage, harda wadansu daya daga cikin manyan ma’aikatanta dake lura da kasuwancin duniya a babban Hedikwatarta. 

Kamfanin Danone ana bayyana shi a matsayin babban kamfani na duniya da yake samar da madarar yogot, wanda rahotanni suka ce kamfanin ya dauki wannan matakin ne na rage ma’aikata a wani mataki na bunkasa ribar da yake samu sakamakon durkushewar da suka alakanta shi da annobar cutar korona, wanda suka ce bullar cutar ya durkusar da tattalin arzikinsu. 


Kamfanin a ranar Litinin din nan yana kuma nazarin mayar da babbar Hedikwatarsa zuwa kusa da birnin Paris na kasar Faransa. Wanda suka ce za su rika tsimi da tanadin Dala Biliyan 1.2 duk shekara zuwa shekarar 2023 idan sun dauki wannan matakin. 

Wadansu bayanai sun ce idan kamfanin ya yi nasarar korar wadannan ma’aikatan na sa, kamfanin ya rasa kashi biyu na ma’aikatansa. 

Idan ba ku manta ba, a watannin baya wata jaridar barkwanci a Faransa da ake kira Charlie Hebdo ta yi wani zanen barkwanci ga fiyayyen Halitta Manzon Allah (SAWW), wanda hakan ya fusata al’ummar Musulmi a duk fadin duniya, inda aka gudanar da gangami da zanga-zanga a kasashen Musulmi daban-daban. 

Sannan kuma aka yi kira ga al’ummar Musulmi su kauracewa kayayyakin da yake da alaka da Faransa, wanda Musulmi suka amsa wannan kiran, lamarin da wasu suke ganin hakan na daya daga cikin dalilan da ya jawo wa wannan kamfani na madara durkuso har yake son ya kori ma’aikata fiye da dubu biyu domin rage kudaden da yake kashewa.


Post a Comment

0 Comments