Boko Haram Guda Uku Ce, In Ji Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taba dora alhakin ta’addancin Boko Haram akan gwamnatin tarayya, inda ya ce gwamnatin tarayya ke da hannu a Boko Haram. 

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan rediyon Muryar Amurka, sai Madogara TV ba ta tantance ko a wacce shekarar ne aka yi hirar da shi. Amma ta lura da hirar ta dade da yinta. Wakilinmu shi ne ya nakalto wani bangare na hirar kamar haka; 

Shugaba Buhari ya ce; “wata uku baya na fadi na ce Boko Haram guda uku ce; da ta asali ta su Muhammadu Yusufu. Da ta kuma Barayi- ‘yan fashi da makami. Alal misali abin da ya faru a Azare, wadanda ma’aikantan Banki, barayi da ‘yan sanda suka hada kai suna fasa bankuna suna daukar kudi suna rabawa su ce Boko Haram ne. Da kuma su gwamnatin tarayyar, ‘yan ta’addan na su, su kashe mutane, gwamnatin su ce ba su bane. To, su wane ne? Sun ce su ne, kuma yanzu shari’a ta same su sune suka yi. Abin da muke ciki yanzu ke nan a kasarnan”. 

Ya ci gaba da cewa; “kuma kowa ya sani yanzu ai. Wannan nauyi na dora shi akan gwamnatin tarayya, saboda gwamnatin tarayya; su wa ke da ‘yan sanda? Su wa ke da shari’a? Su wa ke da sojojin kasa, da na sama da na ruwa? Su wa ke da masu shari’a?”. In ji Buhari. 

Madogara TV ba ta tantance ko a wacce shekarar ne gidan rediyon Muryar Amurka ta yi hira da Buhari ba, amma hirar ya nuna dadaddiya ce. 

Post a Comment

0 Comments