CI GABA DA RIKE HAFSOSHIN TSARO: Buhari Ya Karya Dokar Nijeriya –Sanata Ibrahim ShekarauTsohon Gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce Shugaban kasa Buhari ya karya dokar Nijeriya sakamakon ƙin sauya manyan hafsoshin tsaron Nijeriya da wa'adinsu ya ƙare tun tuni.

A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels, ya bayyana cewa a kundin tsarin mulkin Nijeriya, idan ma'aikaci ya kai shekara 60 da haihuwa ko kuma shekara 35 yana aiki, dole ne ya yi ritaya.

Sanata Shekarau ɗan jam'iyyar APC ne, daga jihar Kano, jihar da ta fi kowace ruwan ƙuri'u ga Shugaba Buhari.

Post a Comment

0 Comments