Dalilin Da Ya Sa Trump Ya Yi Watsi Da Tallafin Korona

Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci majalisun dokokin kasar biyu da su yi wa kudurin dokar tsawaita shirin tallafa wa Amurkawan da annobar coronavirus ta tagayyara tattalin arzikinsu garambawul.

Trump ya bayyana haka ne bayan yin watsi da kudurin dokar tsawaita shirin tallafin da hadin gwiwar majalisun na Amurka suka gabatar masa da ya kunshi Dala biliyan 900.

Daga cikin dalilan da suka sanya Trump yin watsi da kudurin shirin tallafin zango na biyu, akwai ware miliyoyin Dala wajen taimaka wa wasu kasashe a maimakon kaso mafi tsoka na kudaden ya tafi ga Amurkawa.

Karkashin shirin tsawaita tallafin ragewa Amurkawa radadin tasirin cutar coronavirus, za a bai wa kasar Cambodia tallafin Dala miliyan 85, Dala miliyan 134 ga Burma, sai kuma Dala biliyan 1 da miliyan 300 ga Masar, sai kuma Dala miliyan 25 ga Pakistan, yayin da Costa Rica, El Salvador, Guatemala, Honduras, Nicaragua da kuma Panama, za su lakume Dala miliyan 505 daga cikin Dalar biliyan 900 da aka ware don tallafa wa kamfanoni, masu kananan san’o’i, ma’aikata da kuma sauran iyalan da annobar korona ta shafi tattalin arzikinsu a Amurka.

Post a Comment

0 Comments