‘Dan Majalisar Da Ake Zargi Da Rashawa Ya Koma APC

Daga Muhammad Farouk

Dan majalisa Hembe daga jihar Binuwe mai wakiltar Vandeikiya/Konshisha, ya bar jam’iyyarsa ta APGA inda ya koma jam’iyyar APC. Dan majalisar dai a cikin shekarar 2012 an taba zarginsa da karbar rashawa na naira miliyan 30.

Hembe dai ya bayyana komawarsa APC ne a cikin wata takarda da mataimakin Kakakin majalisar, Idris Wase ya karanta a gaban majalisar a yau Talata.

Majiyarmu ta shaidawa Madogara TV cewa, dan majalisa Ndudu Elumelu, da yake kalubalantar ficewar Hembe daga APGA zuwa APC, ya nemi mataimakin Kakakin majalisar da ya ayyana kujerar dan majalisar a matsayin babu mai ita. Inda ya kafa hujja da wasu dokoki daga kundin tsarin mulkin kasarnan. Kudurin da aka yi watsi da shi.

Komawar Hembe zuwa APC ba shi sauya sheka na farko ba a majalisa ta Tara, inda PDP ta rasa ‘yan majalisarta har guda biyu. A majalisar da ta gabata, kotun daukaka kara ta dakatar da wakilcin Hembe a majalisar.

Bayanan da Madogara TV ta samu daga majiyarmu na nuni da cewa; a shekarar 2012 an taba zargin Hembe da karbar na goro har naira miliyan 30 daga hukuma  ‘Securities and Exchange Commission’.

Babban Daraktan Hukumar, Arunma Oteh ya ce Hembe da wasu membobin kwamitin sun kwashi kudi ba bisa ka’ida ba daga hukumar da sunan halartar taro a Jamhuriyyar Dominican, wanda daga karshe suka ki halartar taron. Bisa wannan, Kakakin majalisar a wancan lokacin, Aminu Tambuwal ya kori Hembe a matsayin shugaban kwamitin hukumar.

Sai dai daga karshe hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta kasa gabatar da Hembe a gaban kuliya.

Post a Comment

0 Comments