‘Dan Nijeriya Zai Auri Ba’amurkiya ‘Yar Shekara 46

Wani matashi mai suna Suleiman Isah a karshe an sanya ranar aurensa da masoyiyarsa mai suna Janine Sanchez, wanda za a daura aurensu a ranar 13 ga watan Disamban 2020 a Masallacin Juma’a dake Barikin MOPOL dake Panshekara. 

Maa’uratan ne dai sun hadu ne a shafin sada zumunta na Instagram, inda Sanchez ta baro birnin California na Amurka ta zo Nijeriya a cikin watan Janairun 2020 domin haduwa da masoyinta. 

A yayin ziyararta Nijeriya, Sanchez ta shaidawa manema labarai a Kano cewa; sun hadu ne a shafin Instagram, inda kawai ta ji ya burgeta saboda kirkinsa. “ya aika min da sakon gaisuwa”. 

Ta ci gaba da cewa; akwai wani da yake mata sako, kuma Isah ya san wancan dan damfara ne, sai Isah ya ce masa; “ka nemi sana’a ka daina cutar mutane”, sai Sanchez ta ce; “daga nan kawai na ji cewa (Isah) mutumin kirki ne”. 

Iyayen Isah tuni suka sanyawa ma’auratan albarka a ziyarar da ta kawo Kano, inda suka sanyata ta yi alkawarin cewa za ta bar dansu ya yi karatu a Amurka bayan aurensu. 

Annobar cutar korona tunda farko ya shafi ranar aurensu saboda takaita zirga-zirga da aka yi. Sanchez tana da gidan abinci, kuma tana da ‘ya’ya biyu da mijinta na farko da suka rabu. Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa; tuni Sanchez ta kamo hanya daga Amurka zuwa Kano a shirye-shiryen aurensu. 

“A yanzu haka tana kasar Habasha, muna tunanin isowarta Kano nan ba da jimawa ba”. Tuni aka buga katin gayyatar aurensu, inda aka fara yadawa.
-Rahoton Madora TV

Post a Comment

0 Comments