Duk Da Matsalolin Tsaro A Borno, An Samu Sauki A Mulkin Buhari, In Ji Gwamna Zulum

Gwamna Zulum ya shaida wa tawagar kungiyar Dattawan Arewa, wadda shugaban kwamitin gudanarwarta, Shehu Malami, ya jagoranta zuwa Maiduguri, cewa an samu ingantuwar tsaro a karkashin jagorancin Shugaba Buhari.

A cewar gwamnan, idan aka yi la'akari da halin tsaron da kananan hukumomin jihar 27 suke ciki tun daga 2011 zuwa yanzu, za a iya cewa gwamnatin Buhari ta fi wadanda suka gabace ta a yanayin wanzar da tsaro.

Post a Comment

0 Comments