Duk Da Yajin Aiki ASUU Jami’ar PLASU Za Ta Koma Karatu

Daga Muhammad Farouk 

Jami’ar jihar Filato, PLASU dake garin Bokkos a ranar Talata sun fara yi wa sabbin dalibai da tsoffi rijista a shirye-shiryen janye yajin aiki da kungiyar Malaman jami’o’i wato ASUU ke ci gaba da yi. 

Magatakardar Jami’ar, Amos Mallo, shi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a garin Bokkos, inda ya shawarci dalibai da su bayar da hadin kai wajen yin rijistar. 

Amos ya tabbatar da cewa; za a fara rijistar ne daga ranar 8 zuwa 31 ga watan Disambar 2020. Magatakardar ya shawarci dalibai akan su bi ka’idojin kariya daga cutar korona kamar yadda NCDC suka gindaya domin kaucewa kamuwa da cutar korona.


Post a Comment

0 Comments