Farfesa Zulum Ya Rabawa Iyalai 48 Da Boko Haram Suka Kashe Kudi

 Daga Muhammad Farouk 

Akalla iyalai 48 na manoman da aka kashe a kauyen Zabarmari a jihar Borno suka samu zunzurutun kudin da ya kai naira dubu dari shida kowannensu da kuma kayayyakin abinci daga hannun kwamitin da gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kafa. 

Kowanne iyali, gwamnan ya gwangwaje su da naira 600, 000 da kuma kayayyakin abinci domin rage musu radadin rashin iyalansu. 

Kudin wanda kungiyar gwamnonin arewa suka bayar da gudummawar naira miliyan 20, a yayin da kuma Hukumar lura da ci gaban arewa maso gabashi, NEDC suka bada gudummawar naira miliyan biyar.

Kwamitin wanda kwamishinan matasa da wasanni, Saina Buba ya jagoranta, sun raba kudin ne da kayayyakin abincin ne a yau Alhamis ga iyalan wadanda harin Zabarmari ya shafa.

Kauyen Zabarmari yana Jere ne a tsakiyar jihar Borno. 

Kayayyakin abincin da aka raba musu ya hada da shinkafa, masara, wake, mai, magi, tumatur, da kuma gishiri, wanda ma’aikatar jin kai ta bayar domin a bai wa iyalan kamar yadda kwamitin Buba ya tabbatar. 

Buba ya tabbatar da cewa ba an bai wa kowanne iyali naira dubu dari shida a matsayin diyyar rayukan wadanda suka rasa bane, kawai an ba su kudin ne domin rage musu radadin rashin ‘yan’uwansu wadanda suka kasance jigo a rayuwarsu da iyalansu.

Post a Comment

0 Comments