Gwamna Matawalle Ya Zargi Yari Da Tayar Da Rikici A Zamfara

Daga Muhammad Farouk

Zargin da kare kai daga zargi na ci gaba da tashi a tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da tsohon gwamnan jihar Abdul’aziz Yari. 

Gwamnan jihar, Bello Matawalle ya zargi tsohon gwamnan jihar, Abdul’aziz Yari da hannu wajen rikicin da ya auku wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutum biyu dangane da zaben kananan hukumomi a jihar. 


Gwamna Matawalle ya ce Abdul’aziz Yari ya dira a karamar Hukumar Bakura domin kamfen tare da rakiyar ministan ‘yan sanda, domin tada rikici; “hakan ya sanya na janye zuwa Bakura da na yi niyyar yi domin kaucewa rikici”. 


Matawalle ya zargi Yari da rashin mutunta rayuka domin cimma manufa. Ya ce; Abdul’aziz Yari yana tare da ministan ‘yan sanda a Bakura a yayin da aka kashe mutum biyu ciki harda wani da ake kira Muhammad Sani, tare da raunata da daman gaske. 


Matawalle ya ce ya kira Yari da ya janye zuwansa Bakura domin kamfen, inda ya bukaci ya bar al’umma su zabi wanda suke so ba tare da katsalandan ba. Ya zargi Yari da ikirarin cewa PDP ba za ta ci zabe ba a jihar, wanda ya ce; “idan kana da tabbacin haka me yasa kake neman daukin gwamnonin Kogi, Jigawa, da kuma Kebbi? Da kuma taimakon Sanatoci biyar da shugaban masu rinjaye na majalisa?” ya tambaya. 


Sai dai shugabancin jam’iyyar ya yi watsi da zargin cewa sun tada rikici a jihar, inda suka ce PDP ce ta kawo ‘yan daba domin a kai wa membobinsu hari, inda APC ta ce PDP ta san cewa ba za ta ci zabe ba shiyasa ta yi hakan. 


APC ta ce tuni ta kai kara wajen Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, da kuma shugaban DSS, kamar yadda Liman Kaura, shugaban APC na jihar ya tabbatar. 


-Rahoton Madogara TV

Post a Comment

0 Comments