Gwamnatin Katsina Ta Haramtawa Malamai Amfani Da Facebook Da 'WhatsApp Group'

Daga Muhammad Farouk

Gwamnatin jihar Katsina ta bai wa dukkanin shugabannin makarantu da su goge zaurukan WhatsApp da Malamansu ke amfani da su a makarantun gwamnatin jihar. 

Gwamnatin Katsina ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Muhammad Sada Dikko ya sanyawa hannu a madadin shugaban sashe na ma’aikatar ilimi ta jihar, inda ya zargi zaurukan shafukan sada zumunta wajen amfani da su wajen kin bin umurnin gwamnati da kawo zagon kasa. 

“an ba ni umurnin na sanar da dukkanin shugabannin makarantun gwamnati da su shaidawa shugabannin zaurukan WhatsApp na makarantunsu su goge zaurukan na su da suke kan manhajar WhatsApp”. Inji sanarwar. 

Sanarwar ta ci gaba da cewa; rushe zaurukan WhatsApp ya zama wajibi sakamakon irin rubututtukan da ake tura wa wanda yake haifar da zagon kasa da bijirewa shugabannin makarantu a tsakanin Malaman makarantar. 

Sannan sanarwar ta ce an shawarci shugabannin makarantun da su tuna wa Malaman dokar haramta musu bayyana ra’ayinsu mai kyau ko mara kyau ga gwamnati a shafukansu na Facebook da WhatsApp.

Post a Comment

0 Comments