Hikayata 2020: Maryam Umar Ce Gwarzuwar Gasar

 


Ta yi nasara ne da labarinta mai taken; 'Rai da Cuta'. Maryam Umar ta samu kyautar kudi dala dubu biyu wato kusan Naira miliyan daya kenan.

Surayya Zakari Yahaya ce ta zo ta biyu da labarinta mai suna 'Numfashin Siyasata' kuma ta samu kyautar kudi dala dubu daya sannan Rufaida Umar Ibrahim ta zo ta uku da labarinta mai suna 'Farar Kafa' da kyautar kudi dala dari biyar.

An karrama marubutan ne a wani bikin da BBC Hausa ta shirya a Abuja.


Maryam Umar na karbar kyautarta ta Dala Dubu Biyu A Abuja


Wannan ne karo na biyar da Sashen Hausa na BBC ke karrama gwarazan gasar ta rubutun gajerun labarai ta mata zalla.

Labarin Rai da Cuta ya duba yadda mutane ba su yarda da cutar korona ba, cutar da ta zama annoba a duniya.

Tauraruwar labarin mace ce mai juna biyu da mijinta ya kamu da cutar korona amma ya ƙi kai ta asibiti har ita ma ta kwashi cutar.

Mijin nata ya kulle ta a ɗaki har ta kusa rasa ranta sannan jaririn da ke cikinta ya mutu kamar yadda rahoton BBC Hausa ya labarto. 


Post a Comment

0 Comments