ICC Za Ta Fara Binciken Laifukan Yaƙi Da Aka Aikata A Nijeriya

Rahotanni sun bayyana cewa; babbar mai shigar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC ta ce za ta buƙaci a yi cikakken bincike game da yiwuwar aikata laifukan yaki da cin zarafin bil’adama da aka yi a Nijeriya.

Fatou Bensouda ta ce ofishinta ya kammala nazari sannan ya gano wasu bayanai cewa ƙungiyar ta Boko Haram da sauran ɓangarorinta suna ci zarafin bil’adama. Kuma ta ce daga cikin laifukan sun hada da kisa da fyaɗe da auren dole da kuma azabtarwa.

Bensouda ta kuma ce binciken da za ICC za ta gudanar ya shafi har da jami’an tsaron na Nijeriya.

Post a Comment

0 Comments