Imaan Sulaiman-Ibrahim Ta Zama Sabuwar Shugabar Hukumar NAPTIPDaga Muhammad Farouk

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tabbatar da nadin Imaan Sulaiman-Ibrahim a matsayin sabuwar Daraktar Hukumar dakile safarar mutane ta kasa, NAPTIP. 

Kakakin shugaban kasar, Garba Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata. Inda ya ce Imaan ‘yar asalin jihar Nasarawa ce wacce take da digirinta na farko a bangaren sanin halayyar dan Adam, inda kuma ta yi digirinta na biyu a bangaren gudanarwa da kuma bangaren sha’anin kasuwanci. 

Har ya zuwa nada ta a wannnan mukamin, memba ce a kwamitin farfado da tattalin arzikin jihar Nasarawa, kuma mashawarciya ce a bangaren sha’anin sadarwa a ma’aikatar ilimi ta jihar.

Post a Comment

0 Comments