Allah Ya Yi Wa Dalibar Jami’ar ABU Rasuwa

Dalibar ABU da ta rasu daga dama.


Allah ya yi wa Safiya Shehu rasuwa. Safiya daliba ce a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, inda take aji 300L tana kuma karantar fasahar sarrafa gilashi wato ‘Glass and Silicate Technology’ a jami’ar.

An bayyana Safiya a matsayin mutum mai mutunci da karamci da kuma tausayi. Ta rasu ne a ranar Larabar 2 ga watan Disamban 2020. 

Madogara TV ta labarto cewa; Safiya it ace shugaban kwamitin yi wa dalibai bitar karatu na sashen da take karatu. 

Muna addu’ar Allah ya jikanta da Rahama. Ya sa aljanna makoma. Aameen. 


Post a Comment

0 Comments