Iran Da Saudiyya Sun Yi Allah-Wadai Da Kashe Manoma A Nijeriya

 


Daga Khadeeja Muhammad 

Kasar Iran ta yi tir da kashe manoma akalla 110 da Boko Haram suka yi a kauyen Zabarmari dake jihar Borno. Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh ya ce Iran na tir da wannan harin ta’addancin kan manoman. 

Inda kuma ta mika ta’aziyyarta ga gwamnatin Nijeriya, al’ummar kasar da kuma iyalan da abin ya shafa. 

Haka zalika kuma a bangare guda, Saudiyya ta yi Allah-wadai da kisan. Ta bayyana hakan ne cikin wani saƙon da ta wallafa a shafinta na Twitter, inda ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta ce abin takaici ne yadda mahara ke kai wa fararen hula hare-hare waɗanda ba su ji ba basu gani ba. Sannan ta isar da sakon ta'aziyyarsu ga iyalan waɗanda aka kashe da kuma gwamnati da kuma ɗaukacin al'ummar Nijeriya.

Bahrain ma ta miƙa irin wannan ta'aziyya ga Nijeriya tana mai fatan ganin an kawo ƙarshen irin waɗannan hare-hare a kusa.

Post a Comment

0 Comments