Jami'ar NOUN Ta Yi Sabon Shugaba

 

Budaddiyar Jami’ar Nijeriya, NOUN, ta yi sabon shugaba, inda Farfesa Olufemi Peter ya canji Farfesa Abdalla Uba Adamu.

Peter, Farfesan sinadarai ne, inda a ranar Alhamis aka ayyana shi a matsayin sabon shugaban jami’ar kamar yadda Daraktan watsa labarai na jami’ar, Ibrahim Sheme ya fitar a wata sanarwa da ya sanyawa hannu. 

A cewar sanarwar, Farfesa Peter ya buge abokan takarar shida kafin ya cimma nasara. Kuma kafin ayyana shi a matsayin sabon shugaba, shi ne mataimakin shugaban Jami’ar. 

Farfesa Peter dai yana da shekara 64 a duniya, kuma dan asalin jihar Ogun ne. Kuma mukamin nasa zai fara aiki ne daga 10 ga watan Fabarairun 2021 bayan Farfesa Abdallah Uba Adamu ya kammala.

Post a Comment

0 Comments