JNI Ta Zargi Shugaba Buhari Da Sakaci A Kashe Manoma A Borno

Daga Muhammad Farouk 

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta nemi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta yi maza ta dauki matakin gaggawa wajen dakile matsalolin tsaro da ake fama da shi a kasarnan. 

Bayanin JNI din ya biyo bayan kashe manoma 43 da Boko Haram ta yi a jihar Borno, inda JNI ta koka da cewa Nijeriya yanzu ta zama kamar kwata babu kwanciyar hankali. 

Madogara TV ta labarto Sakataren kungiyar, Dr Khalid Aliyu, na bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna, inda ya ce ‘yan Nijeriya ba su bukatar komai daga gwamnati illa su dauki matakan da suka dace wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa, ba kawai su tsaya a Allah-wadai ga hare-haren da ake kai wa a sassa daban-daban na kasarnan ba.

Sanarwar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi aikin da yake gabanta na kare rayuka da dukiyoyi, inda ya ce ‘yan Nijeriya sun fi bukatar aiki fiye da surutai. 

JNI dai ita ma ta yi Allah-wadai da kashe-kashen ba tare da jami’an tsaro sun kai hari ba.

Post a Comment

0 Comments