Daga Muhammad Farouk ‘Yan shi’a almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky sun bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaba mara tausa...
Daga Muhammad Farouk
‘Yan shi’a almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky sun bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaba mara tausayi. Sun bayyana hakan ne a wata sanarwa da Abdullahi Musa, Sakataren Dandalin dalibai na ‘yan’uwa Musulmi ya sanyawa hannu kuma Madogara TV ta sami kwafin takardar. Inda ya ce kashe manoma 43 da aka yi a jihar Borno, ya nuna cewa gwamnatin Nijeriya ta gaza wajen yin aikinta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
‘Yan’uwa Musulmin da
aka fi sani da ‘yan shi’a sun caccaki shugaba Buhari bisa sakacinsa da kin kawo
karshen matsalolin tsaro da kashe-kashe da yake addabar kasarnan daga ‘yan ta’adda
da ‘yan bindiga.
A cewar sanarwar, ta
kara da cewa; “rahoton da ke nuni da kashe manoma fiye da arba’in a kauyen
Zabarmari dake karamar hukumar Jere a jihar Borno da Boko Haram suka yi a ranar
Asabar din 28 ga watan Nuwamban 2020, abin takaici ne da Allah-wadai”. Inji sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da
cewa; “wannan kisan kiyashin ga wadanda ba su ji ba ba su kuma gani ba al’amari
ne rashin tausayi ga bil’adama. Kowacce rai akwai bukatar ba ta kariya da
girmamata, abin da aka gaza yi wa wadanda aka kashe ke nan”.
‘Yan shi’ar sun ci gaba
da cewa; ci gaba da tabarbarewar tsaro a kasarnan, musamman a arewacin Nijeriya
alama ce ta rashin shugabanci da gazawa daga wadanda suke jagorantar kasar. Wanda
suka bayyana shugaba Buhari a matsayin mutum marasa tausayi kuma; ‘shugaba mara
bin doka da oda’.
“a lokacin da muke tir
da kashe wannan bayin Allah manoma, muna kuma mika sakon ta’aziyyarmu ga
iyalai, da kuma al’ummar jihar Borno da ma ‘yan Nijeriya baki daya bisa wannan
ibtila’I”. in ji su.
Sun karkare da cewa;
abin takaici ne a ce wadanda suke shugabancin kasarnan ba su da hankali, da
kwarewa, sannan bas u girmama rayukan ‘yan Adam. “sun fi kwarewa ne kawai wajen
kai wa raunana hari, da kashe wa da kuma kama masu zanga-zangar lumana da suke
kiran gwamnati ta yi abin da ya dace”. In ji su.
No comments