Kotu Ta Daure Mutum Biyu Bisa Zargin Kashe Wani Tsoho Dan Shekara 70


Daga Muhammad Farouk

Kotu ta daure wani matashi mai suna  Funmilayo Asogba dan shekara 18, da kuma Kehinde Adeogu dan shekara 22 bisa zargin kashe wani Tsoho mai shekaru 70 a duniya.


Kotun ta tura su gidan yari ne a matsayin ajiya a ranar Litinin din nan bayan ta ki amincewa da rokonsu. Inda ake zarginsu da laifin kisan kai. 


Mai shari’a Linda Balogun ta bada umurnin a ci gaba da tsare su bisa shawarar ofishin shigar da kararraki na jihar Legas kamar yadda sashen binciken manyan laifuka dake Panti a Yaba dake Legas din ya tabbatar. 


Balogun ta dage shari’ar har zuwa ranar 12 ga watan Janairun 2021 domin fara sauraren shari’ar.


Mai gabatar da karar, Insfekta Modupe Olaluwoye tunda farko ya shaidawa kotun cewa; wadanda ake zargi sun hada baki ne suka kashe Oyenuga Rabiu a ranar 5 ga watan Nuwamba a gida mai lamba 7, Justice Eniola Crescent, Ikorodu, Legas. Inda ya ce wadanda ake zargin mutum biyu sun hada baki ne da wasu mutum biyu da suka gudu yanzu haka ake nemansu ruwa a jallo wajen kashe tsohon. Inda suka sace masa kayayyaki masu tsada. 


Sauran mutum biyun da suka gudu sune Joseph da Abiodun, wanda suka sace kudi da kayayyakin alatu na mamacin. 


Laifin na su da ake zarginsu ya sabawa sashe na 223 da na 221 na aikata manyan laifuka na dokokin Legas ta 2015.


Post a Comment

0 Comments