Kotu Ta Garkame Maina A Kurkukun Kuje

Daga Khadeeja Muhammad

Mai shari’a Okon Abang na babbar kotu dake Abuja ya bada umurnin a kai Abdulrasheed Maina gidan gyaran hali dake Kuje a birnin tarayya Abuja. 

A yayin da aka dawo shari’ar a ranar Juma’a, Lauya mai wakiltar Maina, Adaji ya janye daga ci gaba da wakiltar wanda yake karewa, inda sabon mai wakiltar Maina din ya nemi da a dage shari’ar domin hakan ya ba shi damar bin diddigin tuhumar. 

Mai shari’a Abang ya bai wa Lauyan Maina wannan damar, inda ya ce wanda ake karar ya musanta zarge-zargen da ake masa wanda doka ta bada damar ya kare kansa. 

A karshe mai shari’ar ya dage shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Disamba domin ci gaba da shari’ar. 


Post a Comment

0 Comments