Mafi Yawan Mutanen Arewa Munafukai Ne Kuma Makwadaita, In ji Hajiya Naja'atu Bala Muhammad

 

Daga Muhammad Farouk 

Fitacciya kuma gogaggiyar ‘yar siyasarnan, Hajiya Naja’atu Muhammad ta caccaki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, inda ta ce tabbas gwamnatin ta ba su kunya kuma a baibai gwamnatin take tafiya. Sannan ta bayyana ‘yan arewa a matsayin munafukai kuma matsorata kuma makwadaita. 

Ta bayyana hakan ne a yayin hirarta da gidan Rediyon RFI Hausa. Wakilin Madogara TV ya rubuta muku cikakken hirar da aka yi da ita. Ga hirar na ta ne kamar yadda yake: 

“Dokar farko a tsarin mulkinmu shi ne kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Gwamnati a duk duniya ma babban aikinta shi ne wannan. Idan wannan gwamnatin (kowacce gwamnati ce) ta kasa kare rayuka da dukiyoyin al’umma, ba gwamnatin ba hukuma, ba ta da amfani.”.  

“Saboda haka wannan gwamnatin ba ta yi wa al’umma amfanin komai ba don ta kasa kare musu dukiyoyinsu da rayukansu”. 

Hajiya Naja’atu ta ci gaba da cewa; “ba a rasa (masu fada mata gaskiya ba), ko mu muna fada. Yanzu ma fada muke, amma mafi yawa musamman mutanen arewa, shiyasa ran mutumin arewa ya zama ba shi da amfani. Mafi yawan mutanen Arewa munafukai ne, mafi yawansu matsorata ne, mafi yawansu makwadaita ne! Ka gani da shugabanninsu da Sarakunansu mafi yawa, da Malamansu mafi yawa wadanda da sune aka dogara da ma’aikata da ‘yan siyasarsu. ‘Yan siyasarsu banda tumasanci da karya da sata ba sa komai. Sun shiga siyasa ne ba don al’umma ba sai don su cika aljihunsu. Ana kashe ‘yan arewa kamai kiyashi. Banda a arewa ba inda za a yi wannan a zauna lafiya”. 

“Mutane da yawa suna kallon Malamanmu a matsayin shugabanni, amma yanzu ka ga wannan ta kau. Malamai aikinsu idan siyasa ta zo, shi ke nan a ba su su je su yi babatu su ce a zabi wanda dai ya ba su kudi, babu Allah a gabansu. Shiyasa za ka ga da a ce mutum yana kuka an karkashe musulmi, yau ya yi shiru ya siyar da imaninsa ga wulakantacciyar riba, tir da su. Sun yi asara. To, su karan kan su Talakawan, ya kamata su gane cewa su fa marayu ne”. 

“Gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta tausayin al’umma, musamman al’ummar arewa, saboda sun yi shiru. Duk idan ka yi shiru ka yarda ke nan. Kashe mutane shi ne kudi a wurin sojojin Nijeriya, shi ne kudi a wurin ‘yan sandan Nijeriya. Saboda haka idan da shugaba Buhari ya damu, da yanzu ya yi tankade da rairaya a cikin sojojin. Saboda haka ni abin da nake gani; yanzu abin da ya kamata ‘yan arewa su yi yanzu abu guda biyu ne. Na farko; mu rijiba a kan mai kowa mai komai wanda zai iya saka mana. A koma da istigfari da gaskiya akan ya yi mana sakayya, ya kubutar damu. Ya halaka wadannan azzalumai. Domin idan ba halaka su ya yi ba, ba za mu zauna lafiya ba”. 

Hajiya Naja’atu ta kara da cewa; “(yanzu) idan jama’a ba su kare kansu ba za su zauna ne kamar dabbobi? ‘Yan Arewa dole ne shugabanni idan akwai su, su ji tsoron kabari, ka da ku ji tsoron kullewar wani, al’umma mu zo mu hada kai mu kare kanmu. Tuntuni ake cewa shugaba Buhari mulkinsa na kama karya ne, muna rantsuwa muna cewa ba kama karya bane, saboda abin da muka gani. Amma yanzu baibai muka gani”. 

Ta ci gaba da cewa; “ita tuntuni gwiwarta ta yi sanyi, na shiga kurkuku, na wahala, ba abin da ba a yi min ba saboda shi, an sanya min guba, an doke ni, an yi min tsirara saboda shi, amma bai biya ni ba. Ba zai biya ni ba, saboda da ya yi wa al’umma abin da muka yi yaki domin a yi mana shi ne adalci. A raba mu da ta’addanci, a yi yaki akan cin rashawa. Yanzu an kassara kasarnan. Kasarnan ta talauce ba don komai ba saboda ba a taba satar kudaden al’umma tunda muka sani a tarihin Nijeriya kamar wannan lokacin ba. Wasu da yawa sun mutu saboda shi, akwai hakkinmu a kansa. Akwai hakkin jinin al’umma a kan sa”. 

-Rahoton Madogara TV

Post a Comment

0 Comments