Matsalar Tsaro: Deji Ya Gorantawa ‘Yan Arewa

Daga Muhammad Farouk

Fitaccen dan gwagwarmayarnan a shafukan sada zumunta, Deji Adeyanju ya gorantawa ‘yan arewa akan matsalolin tsaro da yake addabar arewacin Nijeriya, inda ya ce har yanzu batun #EndSARS na ci gaba da jan hankalin duniya a shafukan sada zumunta, amma matsalolin tsaron da yake addabar arewacin Nijeriya ba ya jan hankalin duniya. Inda ya ce; “ku tambayi kanku ko me yasa? Zak u sami amsarku”. kamar yadda wakilin Madogara TV ya labarto mana. 

Deji Adeyanju ya bayyana hakan ne a sahihin shafinsa na Facebook. 

A kwanakin nan da suka gabata ‘yan ta’addan Boko Haram suka kashe manoman shinkafa kusan 100 a kauyen Zabarmari dake jihar Borno. 

Inda kuma a ranar Litinin da suka gabata, ‘yan bindiga suka yanka manoma Bakwai a jihar Katsina tare da garkuwa da mutum 30. 

Lamarin tsaron na baya-bayan ya ja hankalin duniya, inda aka rika caccakar shugaban kasa Buhari da ya sauka daga mulkinsa saboda gazawarsa, ko kuma ya kori shugabannnin tsaron Nijeriya saboda sun gaza. Lamarin da shugaban kasar ya yi watsi da batun. 


Post a Comment

0 Comments