Matsalar Tsaro: Gwamnonin Niajeriya 36 Sun Shirya Ganawa Da Buhari


Daga Muhammad Farouk 

Gwamnonin Nijeriya 36 sun shirya ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari nan ba da jimawa domin tattauna kalubalen tsaro da yake fuskantar kasarnan, kamar yadda kungiyar gwamnonin Nijeriyar ta tabbatar. 


Kungiyar ta bayyana hakan ne a takardar bayan taron da suka shirya karo na 22 a Abuja a ranar Juma’a, inda shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya sanya wa takardar hannu. 


A cewar takardar kamar yadda wakilin Madogara TV ya bibiyi takardar da kungiyar ta wallafa a shafinta na Twitter, shugaba Buhari zai yi magana kana bin da ya faru da manoma a jihar Borno. Takardar ta ce gwamnonin sun tattauna akan abin da ya shafi matsalar tsaron kasarnan, musamman ma batun kisan manoman shinkafa 43 da aka yi a garin Kwashebe dake karamar hukumar Jere a jihar Borno. 


Post a Comment

0 Comments