Shugaba Rouhani Na Iran Ya Caccaki Majalisar Kasar

Bangaren zartaswar Iran ya yi tir da wani aikin da 'yan majalisar kasar suka gudanar wanda fadar shugaban kasar ya ce zai nakasa kokarin da take yi na dawo da ci gaban kan batun yarjejeniyar Nukiliyar Iran.

Shugaba Hassan Rouhani na kasar Iran ya bayyana adawarsa da kudurin dokar da majalisar kasar ta amince da shi, inda kudurin zai dakatar da sa idon majalisar Dinkin Duniya kan harkokin makamashin Uranium na kasar.

Gidan Rediyon Jamus ya labarto cewa; ra'ayin shugaban na Iran ne cewa matakin majalisar dokokin kasar zai maida hannun agogo baya a kokarin da ake yi na dawo da yarjejeniyar Nukiliyar kasar da aka cimma a 2015.

Jayayya kan kudurin dokar wanda ya samo karfi bayan kisan wani gwanin kimiyyar Nukiliyar makon jiya a kasar na tabbatar da karfin adawa da ke tsakanin Shugaba Rouhani mai matsakaicin ra'ayi da kuma 'yan majalisar kasar masu tsaurin ra'ayi.

Iran din dai na kokari a yanzu na ganin yadda za a kwance mata takunkuman tattalin arziki da Amurka ta kakaba mata.

Post a Comment

0 Comments