Ta’addanci Ba Zai Kare Ba A Nijeriya Har Ya Zuwa Nan Da Shekaru 20 Masu Zuwa, In ji Burutai

 Shugaban Hafsan sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Burutai ya maida martani ga masu kiraye-kirayen a kore su a mukamansu bisa ci gaba da zubar da jinin ‘yan kasa da ake ci gaba da yi a fadin kasar.Sabunta kiraye-kirayen bayan nan ya biyo bayan kashe manoman shinkafa fiye da 110 da Boko Haram suka yi a kauyen Zabarmari dake jihar Borno.


Sai dai Burutai ya maida martani a ingantaccen shafinsa na Facebook a ranar Talata, inda ya ce ta’addanci zai ci gaba nan da shekaru 20.


“akwai rashin fahimta akan mene ne ta’addanci da ‘yan ta’adda. Akwai yiwuwar ta’addancin da yake aukuwa a Nijeriya ya wanzu nan da wasu shekaru ashirin masu zuwa”.


Ya ci gaba da cewa; “ya danganta da yadda masu ruwa da tsaki da suka da jami’an soji da na farar hula za su tunkari lamarin. Da kuma cikin kasa da kasashen duniya za su fuskanci lamarin”.


“gudummawar ‘yan kasa yana da matukar muhimmancin gaske. Akwai bukatar kowa ya bada hadin kai wajen dakile matsalar tsaron nan. Akwai bukatar hada hannu da karfe wajen yin aikin nan”. Ya tabbatar.

Post a Comment

0 Comments