‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Matashi Duk Da Biyan Kudin Fansa A KadunaDaga Muhammad Farouk

Rahotannin da suke shigowa Madogara TV na nuni da cewa; masu garkuwa da jama’a sun kashe wani matashi mai suna Sani Khalil Digana, duk da amsar kudin fansa da suka yi domin su sake shi.

Rahotanni sun nuni da cewa; an sace Khalil ne a yayin da masu garkuwa da jama’ar suka kai hari a Rigasa, inda suka kashe wani mai suna Rabiu Auwal da raunata Umar Bn El-Khatab. 

An dai sace shi tun ranar 21 ga watan Nuwamba, a titin da ya hada zuwa tashar jirgin kasa dake Rigasa Kaduna. Bayanai a wancan lokacin sun yi nuni da cewa; matasan suna cikin mota a titin a lokacin da ‘yan bindigar suka bude musu wuta. 

Wani dan uwan mamacin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatarwa majiyarmu cewa; masu garkuwan sun kashe Sani bayan da suka karbi kudin fansar.

Post a Comment

0 Comments