‘Yan Bindiga Sun Sace Dan Majalisar Jihar Taraba


Daga Muhammad Farouk 

Wadansu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace Barista Bashir Mohammed, dan majalisar jihar Taraba mai wakiltar Nguroje. 

Wata majiya daga iyalan dan  majalisar wanda suka nemi a sakaya sunansu, sun ce dan majalisar wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar kan harkokin labarai an sace shi ne a gidansa dake bayan filin sallar idin Dr Jalo dake Jalingo da misalin karfe 1:45 na dare. 

Majiyar tamu ta ce; a yayin harin da ‘yan bindigar suka kawo, sun kwashe kusan awa uku ba tare da jami’an tsaro sun kawo dauki ba. 


Post a Comment

0 Comments