‘Yan Bindiga Sun Yanka Manoma Bakwai Da Garkuwa Da 30 A Katsina

 A daidai lokacin da kasa ke ci gaba da jimamin yanka manoma fiye da 110 a jihar Borno, wadansu da ake zargin ‘yan bindiga ne a makon da ya gabata sun yanka manoma bakwai ciki harda uwa mai shayarwa a kauyukan Tashar Bama, Dogun Muazu da kuma Unguwar Maigayya dake karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina.

Dan majalisar jiha mai wakiltar yankin, Honorabul Ibrahim Danjuma Machina ne ya tabbatar da lamarin a gaban majalisar jihar a ranar Litinin, a yayin da yake gabatar da kudurin da yake akwai na sake kai jami’an tsaro wadansu kauyukan dake yankinsa.

Bayan ga wadanda aka kashe, ya tabbatar da cewa; ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutum 30 mazauna kauyukan. A cewarsa da alama ‘yan bindigar sun sauya salon kai hare-hare da dadddare, a yanzu haka da rana suke kai harin kan mazauna kauyukan.

“al’ummarmu suna rayuwa cikin firgici da tsoro tunda yanzu haka ma ‘yan bindigar da rana tsaka suke kai hare-hare a kauyukan”. Ya tabbatar.

Ya ci gaba da cewa; “suna kashe mutanen, su yi awon gaba da dukiyarsu tare da garkuwa da dimbin jama’ar da za su iya”.

 “babu ranar da ‘yan bindiga ba za su kai hari a wani kauyen ba, yanzu haka mutane ba sa iya kwana a gidajensu”. Har wala yau ya bayyana kauyuka uku da ya hada Faskari da Sabuwa a matsayin wata mazauna na ‘yan bindiga a jihar Katsina.

Da suke na su karin bayanin, ‘yan majalisa masu wakiltar Dutsinma da Safana, Mohammed Khamis da Abduljalal Haruna Runka, sun bayyana hare-haren ‘yan bindigar a matsayin ‘tashin hankali’.

A karshe, kakakin majalisar, Tasiu Zango, ya bukaci da a mikawa gwamnan jihar a rubuce bukatar ‘yan majalisar na kai jami’an tsaro yankin domin tabbatar da tsaro a yankunan.

Post a Comment

0 Comments