'Yan Sanda Sun Afka Wa 'Yan Shi'a A Abuja

A ci gaba da fafutikar ganin an saki jagoransu Shaikh Ibraheem Zakzaky da 'yan shi'ar ke yi a kowacce rana a birnin tarayya Abuja, a yau Talata, jami'an 'yan sandan Nijeriya sun afka ma 'yan shi'ar a yayin da suka fito muzaharar da suka saba. 

Mjiyarmu ta shaidawa Madogara TV cewa; 'yan shi'ar sun fara muzaharar ta su ce daga GT Bank dake Kasuwa Wuse inda aka tafi da ita har zuwa Bega kafin 'yan sandan sun tarwatsa su da borkonon tsohuwa.

Ganau sun shaida mana cewa; ba su ga an kama wani ko raunata wani ba.

Post a Comment

0 Comments