Yan Shi'a: Amurka Ta Sanya Nijeriya Cikin Ƙasashen Da Ke Dakile 'Yancin Yin AddiniDaga Wakilinmu Da Kuma BBC Hausa

Gwamnatin Amurka ta sanya Nijeriya cikin jerin kasashen da ke dakile 'yancin gudanar addini ba tare da takura ba. Kasar ta ce Nijeriya tana barazana ga masu son yin addinansu kamar yadda ya kamata.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo, bai bayar da takamaimen dalilan sanya Nijeriya a wannan jeri ba a lokacin da yake sanar da daukar matakin.

Sai dai tun a farko ma'aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana yadda gwamnatin Nijeriyar ta daure ɗaruruwan mabiya Harkar Musuluncin da aka fi sani da ‘yan Shi'a.

Kazalika, ta nuna yadda a wata jihar da Musulmai suka fi yawa aka kama mutanen da suka ki yin azumin watan Ramadana.

Sauran kasashen da Amurka ta sanya cikin jerin masu dakile 'yancin gudanar da addini su ne China da Iran da Pakistan da Myanmar da Koriya ta Arewa da Saudiyya.

Bayanai sun nuni da cewa; kasashen da ke cikin wannan jeri za su iya fuskantar takunkumi daga Amurka idan suka gaza inganta tsarinsu na tabbatar da 'yancin gudanar da addini.

WAIWAYE

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya,
Shaikh Ibraheem Zakzaky

A shekarar 2015 ne gwamnatin Nijeriya ta kama shugaban Harkar Musulunci, Sheikh Ibraheem Zakzaky, a lokacin wani hari da sojoji suka kai masa a gidansa wanda ya yi sanadiyyar kashe mabiyansa fiye da 1, 000 kamar yadda mabiya Harkar ke fadi. 

Sojoji sun zarge su da tare hanya da kuma yunkurin kashe shugaban rundunar sojin kasa ta kasa. Zargin da mabiya Harkar suka sha musantawa. Wanda kuma kotu ta wanke dukkanin wadanda aka kama daga cikin mabiya Harkar aka kuma gurfanar da su gaban kuliya.

Sai dai har yanzu gwamnatin kasar na tsare da Sheikh El-zakzaky duk da umarnin da kotuna daban-daban suka bayar na sakinsa.

Post a Comment

0 Comments