YANZU-YANZU: Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Hukuncin Kisa Kan Maryam Sanda


Daga Muhammad Farouk 

Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja, ta tabbatar da hukuncin kisa ga Maryam Sanda da ta kashe mijinta Bilyamin Mohammed Bello a shekarun da suka gabata kamar yadda Madogara TV suka labarto. 

Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa; gwamnatin tarayya dai ta gabatar da Maryam Sanda da wadansu mutum uku bisa zargin kisan kai. A ranar 27 ga watan Janairun 2020, mai shari’a Yusuf Halilu ya zartar mata da hukuncin kisa. 

A hukuncinsa, Halilu ya ce; “wanda ake zargi ta cancanci mutuwa, a don haka na zartarwa da Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya har sai ta mutu”.

Sai dai Lauyan da yake kare Maryam Sanda bai gamsu da hukuncin kotun ba, inda ya daukaka kara zuwa kotun daukaka kara, inda yake neman da kotun ta sauya hukuncin kotun. Inda ya bayyana hukuncin kotun farko a matsayin “hukuncin rashin adalci”, wanda ya ce hukuncin bai samu wanda ake zargi da amsa zargin ba, ko kuma wata hujja da yake nuna cewa wacce ake zargi ita ce ta kashe mijinta, sannan kuma rahoton gawar bai bayyana hakikanin sanadin mutuwar mijinta ba. 


Post a Comment

0 Comments