Zan Sake Tsayawa Takarar Shugaban Kasa -Trump

Shugaban kasar Amurka mai barin gado Donald Trump, wanda ya rasa goyon baya a  kokarinsa na kalubalantar zababben shugaban Amurka, Joe Biden, ya fito karara yana bayyana muradinsa na sake tsayawa takarar shugabancin kasar a zabe na gaba.

A yayin da yake jawabi ga bakin da suka halarci liyafar Kirsimati da aka shirya a fadar White House, Trump ya bayyana fatansa na sake ganin su a shekaru 4 masu zuwa.

Duk da cewa ba a bai wa ‘yan jarida damar shiga zauren liyafar da ta samu halartar kusoshin jam’iyyar Republican da dama ba, bidiyon jawabin shugaban mai barin gado ya samu kai wa ga al’umma.

Post a Comment

0 Comments