Zargin Handame Miliyan 950: Kotu Ta Wanke Tsohon Minista Ambassada Wali

Daga Muhammad Farouk

Wata babbar kotu a Abuja ta wanke tare da sallamar tsohon ministan harkokin Nijeriya, Ambassada Aminu Wali, da kuma tsohon kwamishinan ayyuka a Kano, Mansur Ahmad bisa zargin da ake musu da halasta haramtattun kudi. 

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa, EFCC, ita ce ta kai mutanen kotu bisa zarginsu da karbar kudaden ba tare da kudin sun bi ta ka’ida ba wanda hakan ya sabawa dokar hulda da kudade na shekarar 2011. 

Da yake zartar da hukunci, Mai Shari’a Lewis Allagoa, ya ce; wadanda suke zargi sun kasa gabatar da gamsassun hujjoji, a don haka an wanke tare da sallamar wadanda ake zargi. 

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Lauyan da ke kare su Wali, Sam Olagunorisa, ya ce sun ji dadi da wannan hukuncin ganin yadda aka wanke wadanda yake karewa. 

A na shi bangaren, Lauyan EFCC, Cosmos Ogwu ya ce; za su yi nazarin hukuncin domin daukar matakin da ya dace a gaba.

Post a Comment

0 Comments