An Saka Ranar Muƙabala Tsakanin Sheikh Abduljabbar Da Malaman Kano

 

Gwamnatin Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta tabbatar wa da BBC cewa ranar Lahadi, 7 ga watan Maris za a shirya muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Jihar.

Kwamishinan Yaɗa Labarai ya ce sun shirya tsaf domin gudanar da muƙabalar.

Shi ma Kwamishinan Harkokin Addini Dr. Muhammad Tahir ya tabbatar da BBC saka ranar.

Tun a ranar 7 ga Fabarairu ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya amince a gudanar da muƙabalar kuma aka faɗa wa ɓangarorin biyu su shirya fuskantar juna a tattaunawar ilimi.

Gwamnatin Kano ta zargi malam Abduljabbar Nasiru Kabara ne da yin "kalaman tayar da fitina game da addinin Musulunci" bayan wasu malamai a jihar sun zarge shi da saɓa wa abin da Musulunci ya zo da shi.

Post a Comment

0 Comments