Ba Don Na Gudu Jamhuriyyar Nijer Ba, Da Yanzu An Yanke Kafa Ta -Abdulrasheed Maina

 

Abdulrasheed Maina

Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban Hukumar farfado da tsarin fensho (PRTT) a ranar Juma’a ya shaidawa Babban kotun Tarayya dake Abuja cewa; ba don guduwa da ya yi zuwa jamhuriyyar kasar Nijer ba, da yanzu an yanke masa kafa.

Ya ce tafiyar da ya yi zuwa jamhuriyyar kasar Nijer, ya je neman maganin kafar ta shi ce. 

Maina ya bayyana hakan ne a yayin da yake neman a sake bayar da belinsa a gaban mai shari’a Okon Abang, inda ya ce an yi wa kafarsa aiki ne domin ceton kafar ta shi daga yankewa. Inda ya nemi kotun da ta taimaka masa ta bada belinsa saboda ya samu ya ci gaba da lura da lafiyarsa  da yake ci gaba da tabarbarewa.

A ranar 20 ga watan Janairun 2021, Maina ya nemi Alkali Abang domin a sake bada belinsa bayan da aka sake cafko shi bayan ya gudu jamhuriyyar Nijer. 

A wannan karon dai yana neman a sake bayar da belinsa ne bisa hujjar rashin lafiya. 

Maina a wata korafi da ya shigar a ranar 24 ga watan Disambar 2020, wanda wani Lauyansa mai suna  Anayo Adibe ya mika wa kotun, inda ya ce bukatar hakan ya zama wajibi ne duba da tabarbarewar rashin lafiyarsa. 

A bukatar neman a sake bada belinsa, Maina ya ce yana da mutanen da za su iya tsaya masa idan har aka bada belinsa. 

A zaman shari’ar da aka yi, Sani Katu, SAN, wanda ya bayyana domin tsayawa Maina, ya ce yana da bukatoci uku da aka gabatar a gaban kotun. Katu ya ce baya ga neman beli da aka yi, ya sake neman bukatar kotun ta rubuta takarda zuwa gidan gyaran hali dake Kuje a Abuja da ta bayar da damar a rika duba lafiyar wanda yake karewa. Inda ya ce gidan yarin ba su da kayan aikin da za su duba lafiyar wanda yake karewa. 

Har wala yau Lauya Katu ya ce wanda yake karewa bada jimawa ba aka kai shi asibitin koyarwa na Jami’ar Abuja dake Gwagwalada, inda ya ce bayanin kai shi asibitin yana cikin bayanin bukatar neman belinsa da ya mikawa kotun. 

Lauyan ya nemi kotu da ta bai wa Maina beli, inda ya bai wa kotun tabbacin cewa wanda yake karewa ba zai yi wasa da wannan damar ba, inda kuma ya ce zai rantse kan hakan. Lauyan ya jaddada cewa maganin da aka yi wa Maina a Nijer ne ya sanya ba a kai ga yanke kafarsa ba. 

Sai dai Lauyan EFCC, Mohammed Abubakar, ya nemi da kotun ta hana bayar da belin Maina. Inda Abubakar ya ce bai gamsu da bayanin Lauyan da yake kare Maina ba, musamman idan aka yi duba da yadda wanda yake karewa ya gudun ma belin farko da kotun ta ba shi. 


A karshe bayan sauraren bayanan kowa, Alkali Abang na kotun ya sanya ranar 25 ga watan Fabarairun nan domin yanke hukunci. 
Post a Comment

0 Comments