Ba A Yi Wa Fulani Adalci A Nijeriya –Isa Yuguda

Tsohon gwamnan Bauchi, Isa Yuguda

Daga Muhammad Farouk

Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mallam Isa Yuguda ya yi tir da kokarin bata sunan Fulani da ake yunkurin yi a Nijeriya.

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan a yayin da yake hira da ‘yan jarida bayan ya sake sabunta rijistarsa a jam’iyyar APC a ranar Litinin a Bauchi, inda ya ce an dade ana nunawa Fulani rashin adalci a kasarnan.

Isa Yuguda ya ce Fulani makiyaya suna samarwa da kasarnan akalla shanu miliyan daya a kullum wadanda ake yankawa domin amfanar al’umma, amma duk da haka gwamnatin tarayya ta yi watsi da sun a tsawon shekaru.

A cewarsa, idan gwamnati za ta saki kudi masu yawan gaske wajen tallafawa bangaren noma, me yasa gwamnati ba za ta bada tallafi a bangaren kiwo ba? Ya tambaya.

“halin ko in kula da ake nuna wa Fulani musamman makiyaya wadanda suke taimakawa Nijeriya da akalla shanu miliyan daya a kullum domin ganin al’umma sun ci nama, amma yadda ‘yan Nijeriya ke mu’amala da su abin takaici ne kuma ba adalci a ciki,”, inji shi.

Ya ci gaba da cewa; “rashin adalci a nan shi ne, a lokacin da Lord Luggard ya gama mallake arewacin Nijeriya, Fulani makiyaya ne kawai hanyar samun kudi. Sun rika samar da haraji wanda ya kawo ci gaban bunkasa bangarori da dama a Arewa ciki kuwa harda jihar Binuwe inda a yanzu ake korar su. Su makiyaya ne, mutane ne da suke samar da nama ga dukkanin kasar, kuma zamu iya kallonsu a matsayin wadanda suke bunkasa bangaren noma da kiwo. An sanya biliyoyi da tiriloyin kudi a wannan bangaren da sunan tallafin taki da sauran su, kun taba jin gwamnatin tarayya ta sanya tallafi a bangaren kiwo?” ya tambaya.

Isa Yuguda ya ci gaba da cewa; “ni abin da nake cewa a nan shi ne; Nijeriya a matsayinta na kasa ba yi wa Fulani adalci. A lokacin da Bature ya zo, ya mutunta su saboda sune suke samar da kudi, ba kawai samar da hanyar shanu daga Maiduguri zuwa Otukpo ba, ko daga Sakkwato zuwa Lokoja da Ilorin, wadannan ci gaba na gine-gine ma wadannan Turawa suka samar da su”.  

“mu daina sanya son rai saboda Allah, idan ba haka ba, kasarnan za ta durkushe, kuma za ta tarwatse ne a hannunmu. Ina jin tsoro, ku ‘yan jarida kune kuke rura wutar rikicin nan. Ya kamata ku ceci kasarnan ko don kanku, kune matasa, idan ba ku yi hakan ba, ba za ku gaji kowacce kasa ba,” ya lurantar.

Post a Comment

0 Comments