Barazanar Korar Fulani Makiyaya: Gwamna Bala Ya Kwankwashi Gwamnan Binuwe

 


Daga Muhammad Farouk 

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, ya kwankwashi gwamnan jihar Binuwe Samuel Ortom da sauran gwamnonin Yarbawa da na Ibo bisa yadda suke tsangwamar Fulani makiyaya sakamakon ayyukan tsiraru daga cikinsu. Inda ya ce ba a kabilantar da miyagun ayyuka domin a kowacce kabila akwai bata gari. 

Gwamna Bala ya bayyana hakan ne a taron da Kungiyar ‘yan jarida reshen jihar Bauchi suka shirya, inda ya ce; “zan fada muku wani abu da na gaya wa ‘yan’uwana (gwamnoni). Dangane da rikicin Fulani makiyaya da manoma a Nijeriya. Kuna ganin abin da ‘yan’uwanmu gwamnoni daga kudu maso yamma ke yi, wadansu daga kudu maso gabas. Wadansu daga cikinmu sun fada musu gaskiya cewa; abin da kuke yi ba daidai bane”, ya tabbatar.

Gwamnan da ya tashi kwankwasar gwamnan Binuwe, ya ce “wanda ya fi kowa kuskure shi ne gwamnan jihar Binuwe, gwamna Ortom. Idan ba ku bai wa kabilar wadansu wuri ba, mu ai muna bai wa kabilun wasu wuri a Bauchi da wadansu wurare. Muna da mutane da dama da suke noma a Alkaleri, suke noma a Tafawa Balewa, suke kuma noma a Bagoro. Shin wani ya taba ce musu su tafi ne? Bamu taba ba! Saboda suna da ‘yancin su kasance a nan”. 

“Muna da Yarbawa a Bauchi suna zaune fiye da shekara 150 tun kafin haihuwar Nijeriya. Babu wanda ya takura musu. Wadansu daga cikinsu sun kai matsayin ma Sakatarorin ma’aikatun gwamnati, a Gombe da Bauchi da Borno”.  

Ya kara da cewa; “amma yanzu saboda Bafulatani yana kiwon shanunsa yadda ya saba a gargajiyance, yana shiga cikin dazuka domin kiwonsu, sai aka samu Barayin shanu rike da bindiga suna kashe shi suna tafiya da dabbobinsu, ba shi da zabin da ya rage masa illa ya rike bindiga kirar AK47 domin bai wa kansa kariya saboda a bayyane yake gwamnati ba ta ba shi kariya. Mene ne laifinsa? Laifin gwamnati ne ma da mutane!”

Da yake wanke Fulani makiyaya daga ayyukan tsirarunsu, Gwamnan ya ce; “ba za ka yi musu kudin goro ba baki dayansu (Fulani) ka ce musu ‘yan ta’adda ne. Saboda a kowacce kabila akwai bata gari, idan an samu wani bata gari a cikin wata kabila, ba a yiwa dukkanin kabilar jam’i wajen nuna su a matsayin bata gari. Akwai bukatar mu rika sanya hankali”, ya lurantar. 

Ya nemi ‘yan jarida da su rika sanya kula wajen rahotanninsu. Su kuma rika bambance tsakanin gaskiya da karya wajen hada rahotanninsu. 

Ya kara da cewa; kowanne dan Nijeriya a kudin tsarin mulkin kasar yana da damar zama a duk inda yake so. Inda ya ce babu wanda yake da ikon korar wani daga wani wuri. Kuma a cewarsa gwamnatin Tarayya ce kadai take da ikon lura da dazukan kasar. 


Post a Comment

0 Comments