Boko Haram Sun Farmaki Sojoji A Sansaninsu Sun Kashe Bakwai A Borno

 

Daga Muhammad Farouk 

Sojojin da lamarin ya shafa sune na Bataliya ta 153 dake karamar Hukumar Marte a jihar Borno. 

Rahotanni sun ce akalla sojoji bakwai ne aka tabbatar da kashe su a mummunan harin kwantar bauna da Boko Haram suka kai a jihar ta Borno. 

Majiyarmu ta PREMIUM TIMES ta labarto cewa; Boko Haram din sun kai harin sansanin sojojin ne da misalin karfe 10 na safe a ranar Litinin. Inda sojojin suka fafata da Boko Haram din domin kare sansanin na su daga harin ‘yan ta’addan Boko Haram din; “sai sun gaza hakan sakamakon irin karfin da ‘yan ta’addan suka zo da shi”, inji majiyar tamu. 

Wannan harin ya sanya sojojin sun bar sansanin na su na Marte sun koma Dikwa, wata karamar Hukumar a jihar, lamarin da ka iya sanya wa Boko Haram su ci gaba da kaddamar da hari a Marte. 

Ya zuwa yanzu, rundunar soji ta shawarci runduna ta ‘Sector 3’ musamman wadanda suke Baga, Cross Kauwa, Kekeno, da Monguno da yankunan da suke zagaye da Marte da su kasance cikin shiri ko ta kwana. 

Harin na ranar Litinin da Boko Haram suka kai a karamar Hukumar Marte ya kasance na uku ke nan a cikin watan nan, kamar yadda majiyarmu ta cikin soji ta tabbatar. 

A ranekun 10 da 15 ga watan Janairun 2021, Boko Haram sun kai hari a wannan sansanin. Wanda har ya zuwa yanzu ba a tantance adadin wadanda aka raunata ko kashewa ba. 

Boko Haram din sun dauki nauyin kai wadannan hare-haren, inda bayan kwanaki kuma sojoji suka murkushe su a yankin. 

Rundunar soji ta Tura Taka Bango, tare da hadin guiwar sojin sama sun yi nasarar tarwatsa manyan makaman Boko Haram din guda bakwai, tare da hallaka ‘yan ta’addan da dama. 

A yayin harin, dubban fararen hula ne suka gudu zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno mai akalla nisan kilomita 130 daga inda suke. 

Kakakin rundunar sojin, Mohammed Yerima, bai ce uffan ba kan hare-haren karshen nan a yayin da majiyarmu ta tuntube shi ta wayar tarho, aika masa da sakon kar ta kwana da kuma ta WhatsApp.


Post a Comment

0 Comments