Boko Haram Ta Yi Wa 'Yan Gudun Hijira Biyar Yankan Rago A Borno

 

Rahotannin dake shigowa MADOGARA na nuni da cewa; akalla 'yan gudun hijira biyar suka rasa ransu ta hanyar yankan rago, inda wasu uku suka bace bat a yayin da Boko Haram suka kai hari kan masu saran itace a Karamar Hukumar Damboa da ke Jihar Borno.

'Yan gudun hijirar sun fita neman itacen da za su yi amfani da shi ne yayin da lamarin ya rutsa da su a ranar Lahadi kamar yadda majiyarmu ta tabbatar.

Wani dan banga a garin na Damboa, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar wa da Aminiya faruwar lamarin.

"Mun samu rahoton batan wasu daga cikin 'yan gudun hijirar, wanda hakan ya sa muka shiga neman su, cikin tafiyar da bata gaza kilomita biyu ba, muka iske gawarwakinsu kwance an musu yankan rago.

"Akwai tashin hankali ka ga dan Adam an masa yankan rago, kuma mutanen nan 'yan gudun hijira ne," cewar majiyar.

Wannan na zuwa ne kasa da awanni 24 bayan Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Manjo-Janar Ibrahim Attahiru ya ba wa sojoji umarnin kwato wasu garuruwa da ke karkashin ikon Boko Harama a jihar.


Post a Comment

0 Comments