DAGA KARSHE: An DaidaitaTsakanin Jami'an KAROTA Da 'Yan A Daidaita Sahu


Biyo banyan zaman gaggawa da aka gudanar tsakanin jami’an KAROTA da kungiyar kwadago da kuma wakilan ‘yan adai-daita an cimma matsaya mai kyau.

Kano Focus ta ruwaito shugaban kungiyar Kwadago na jihar Kano kwamared Kabiru Ado Munjibir ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai ranar Talata a Kano.

Kabiru Ado Minjibir ya ce an cimma matsaya masu tarin yawa da za su taimaka gaya wajen kawo karshen halin da ake ciki.

Matsayar da aka cimma

‘Yan Adai-daita Sahu za su biya harajin N100 kamar yadda doka ta tanada a kullum amma ba kamar yadda ya ke a bayaba.

Duk wanda zai biya harajinsa to dole ne ya yi Remiter  karon farko domin a dauki bayanan sa a adana.

Haka kuma kowanne dan sahu zai biya,  na farko a tsakanin makonnin biyu daga ranar 23 ga Fabrairu.

Haka kuma bayan anyi  biyan farko za a ci gaba da biya na kullum-kullun ta wayar hannu ko kuma ta POS ba kamar a baya ba da sai anje banki.

Haka kuma duk wanda ya ke so zai iya biyan na kwana daya ko na sati ko kuma na wata-wata ko na shekara amma ba dole bane.

Haka kuma yana dag cikin abinda aka cimma, cewar shugabannin masu dan sahu za su yiwa mambobinsu bayani kuma za a janye yajin aiki.


-Rahoton Hausa Kano Focus

Post a Comment

0 Comments