Daga Karshe: Majalisar Dattawar Amurka Ta Wanke Trump Daga Zargin Haddasa Rikici A Capitol

Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump

A ranar Asabar majalisar dattawar Amurka ta wanke tsohon shugaba Donald Trump daga zargin ingiza magoya bayansa su yi bore a majalisar dokokin kasar ta Capitol ranar 6 ga watan Janairu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 5 kamar yadda rahoton RFI Hausa ya tabbatar.

Kashi 2 cikin 3 na ‘yan majalisar 100 ne ake bukatar su bai wa kudurin tsige Trump din goyon baya, amma hakan bai samu ba a kuri’ar da aka kada, inda 57 suka zabi a hukunta Trump, yayin da 43 suka zabi akasin haka.

‘Yan majalisar dokokin Republican 7 sun bi sahun ‘yan Democrat wajen neman a hukunta Trump.

‘Yan jam’iyyar Democrat sun dora alhakin kutsen da ‘yan jagaliya suka yi a ginin Capitol a kan Trump, kuma su na bukatar a yi masa hukunci a game da hakan.

Tun da farko sai da majalisar dattawar Democrat, tare da lauyoyin dake kare tsohon shugaban Amurka Donald Trump suka cimma matsaya ta ci gaba da muhawara kan zargin da ake masa ba tare da an gabatar da shaidu ba.

Trump, wanda tun da ya sauka daga karagar mulki a ranar 20 ga Janairu ya ke gidansa na Florida, ya fitar da wata sanarwa, inda yake bayyana jin dadinsa a game da wanke shi da aka yi, amma kuma ya bayyana sauraron bahasin a matsayin ‘bi- ta – da – kulli mafi girma a tarihin kasar.

Post a Comment

0 Comments