Daga Karshe An 'Yantar Da Daliban Kagara

 

Rahotannin dake shigo mana a halin yanzu na tabbatar da cewa Daliban makarantar gwamnati ta kimiyya ta Kagara dake jihar Neja sun samu 'yanci daga hannun 'yan bindigar da suka yi garkuwa da su. 

Wani babban jami'in 'yan sanda dake cikin tawagar dakile garkuwa da jama'a a jihar, shi ne ya tabbatarwa da majiyarmu, inda ya ce yanzu hakan suna kan hanyarsu ta zuwa garin Minna babban birnin jihar Neja.


Idan ba ku manta ba, a ranar 17 ga watan Fabarairun shekarar da muke ciki, 'yan Bindigar suka je da kayan sojoji suka sace daliban makarantar kwana dake Kagara din. Inda suka sace dalibai 27 da kuma Malamai uku da iyalan Malaman 12. 

Yanzu ana sa ran a koyaushe za su iya isa garin Minna din. 

Post a Comment

0 Comments