Dalibai Mata 317 Ne 'Yan Bindiga Suka Sace A Makarantar Jangebe -Kwamishinan 'Yan Sanda


Kwamishinan 'Yan sanda na Jihar Zamfara, Abutu Yaro ya ce daliabi mata 317 ne ba a gani ba bayan harin 'yan bindigar da suka yi garkuwa da dalibai a Makarantar Sakandiren 'Yan Mata da ke  Jangebe.

Yaro, ya bayyana hakan a ranar yayin da yake ba da tabbacin cewa za su yi dukkan mai yiwuwa wajen kubutar da daruruwan 'yan matan.

Sai dai alkaluman da Kwamishinan ya bayar sun saba da na kimanin dalibai 500 da da wani malamin makarantar da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana.

A ganawar da 'yan jaridu a garin na Jangebe da ke Karamar Hukumar Talata-Mafara ta Jihar, Kwamishinan ya bayyana alhininsa ga al'ummomin yankin.

Ya kuma bukace su da kada su dauki doka a hannunsu ta hanyar kai wa masu ababan hawa hari da suka hada da masu rajin tseratar da su da kuma 'yan jarida. 

“Wajini ne mutane su fahimci cewa gwamnati da jami'an tsaro na tare da su wurin yaki da 'yan ta'adda; shi ya sa yake da muhimmanci a bar jami'an tsaro su gudanar da aikinsu yadda ya kamata don ganin sun kubutar da su daga 'yan bindigar. 

“Muna iya bakin kokarinmu tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro da 'yan sa kai da kuma gwamnatin jiha don ganin an kawo karshen wannan lamari. 

“lna ba ku tabbacin cewa za mu kubutar da dukkan daliban da aka sace,” inji shi.

Wasu mazauna yankin sun bayyana wa Aminiya cewa 'yan bindigar kusan 100 ne suka yi zuga a kan babura suna harbi a iska kafin su kutsa cikin makarantar da misalin karfe 2 na daren Juma'a.

Wani ma'aikaci a makarantar ya ce sun tsinci kansu na tashin hankali, kuma kimanin 60 daga cikin daliban sun tsira, wasu kuma sun buya yayin da 'yan bindigar suka shiga makarantar.

Post a Comment

0 Comments