An sauya wa Jami’ar Jihar Bauchi da ke Gadau suna
zuwa Jami’ar Sa’adu Zungur. Wannan sanarwa ta fito ne a wata takardar da
Kwamishinan ilimi na Jihar, Dakta Aliyu U. Tilde ya sanya ma hannu a jiya Laraba
10 ga watan Fabrairu 2021.
Takardar ta bayyana cewa, an sauya sunan Jami’ar ne
domin raya sunan marigayi Malam Sa’adu Zungur, É—an asalin Jihar Bauchi wanda
yana cikin manyan da suka yi fafutikar samun ‘yanci, kuma É—aya daga cikin ‘yan
gwagwarmayar siyasa da manufofinsu na ci gaban jama’a ta sauya yanayin siyasar
arewacin Nijeriya.
Takardar ta godewa Gwamnan Jihar, Sanata Bala
Muhammad wanda ya taimaka wa ma’aikatar ilimin wurin cika alkawarin da ta yi ga
wakilan iyalan Malam Mu’azu na tabbatar da ci gaba da raya sunan marigayin.
A ƙarshe, takardar ta bayyana wannan rana a matsayin
babbar rana a tarihin ilimi a jihar Bauchi.
0 Comments