Dan Majalisar Tarayya Ya Sabunta Katin Jam'iyyar APC A Funtuwa

Daga Hussaini Ibrahim, Funtua

Dan majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar karamar hukumar Funtua  da Dandume, Honorabul Muntari Dandutse ya sabunta katin jamiyyarsa ta APC a mazabarsa dake layin Magaji da ke cikin karamar hukumar Funtua a jiya Lahadi.

Dan majalisar Honorabul Muntari Dandutse ya bayyana jindadinsa ganin yadda al'ummar yankin Funtuwa suka fito domin raka shi wajen sabunta katin jam'iyyar musamman ma kananan Hukumomin Malumfashi, Sabuwa, Faskari, Kankara, Bakori, Danja Musawa da Matazu.

Honorabul Muntari Dandutse ya kuma tabbatar ma al'ummar mazabarsa da ma wasu kananan Hukumomin da suka nuna masa kauna cewa zai iya kokarinsa wajen ganin ya taimakawa al'umma.

Kuma ayyukan raya al'umma da yanzu haka yake gudanarwa na Tituna Kwalbati da gyaran Makarantu da Masallatai da taimakin marasa lafiya, Honorabul ya tabbatar da cewa, gadar su ya yi kuma zai ci gaba da su da yardar Allah.

A nasa jawabin Shugaban jam'iyyar APC na shiyyar Funtunwa, Bala Musawa ya tabbatar da cewa samun irin Honorabul Muntari Dandutse a majalisar Tarayya sai an tona wajen yi ma mazabarsa ayyukan raya al'umma, kuma a duk fadin Jihar Katsina shi ne ya yi zara, inji Bala Musawa.

Post a Comment

0 Comments